IQNA

Al'ummar Duniya Na Koyi Da Juyin Musulunci Wajen Gwagwarmaya da Azzaluman Duniya

13:13 - February 10, 2009
Lambar Labari: 1742548
Bangaren Siyasa da zamantakewa: Azzaluman Duniya Al'ummar Duniya Na Koyi Da Juyin Musulunci Wajen Gwagwarmaya da Azzaluman duniya.Wannan gwagwarmaya a tsakanin al'umma ana ganinta a lungu da sako na duniya.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a nan Iran Iqna ta watsa rahoton cewa bangaron arewacin Iran day a hada Mazandarean da babul karkashin jagorancin sansanin gwagwarmaya na Imam Mahdio (AF) sun kaddamar da gagaramin buki a ranar litinin na tunawa da nasarar juyin juya halin musulunci a Iran yau shekaru talatin a babban masallacin yankin.

Wannan gagaramin buki an bude shi da karatun Alkur'ani mai tsarki da babban makarancin yankin Pur Husein ya karanto inda a ci gaba da wannan buki Muhsin Hasan Sade Talashi komanan sansanin yan gwagwarmaya na yankin da kuma sakataren rundunar yan sa kai na yankin da iyalan dakarun sa kai da na wadanda suka yi shahada da wadanda suka ji rauni a lokacin yaki sun gabatar da godiya ta musamman da nasarar juyin musulunci a Iran day a cika shekaru talatin da ayau ya kai matsayi da karfi da samun ci gaba ta dukan bangarori tare da taimakon Allah. Daga cikin abin da wadanda suka gabatar da jawabai suka fi maida hankali shi ne jarumintaka da rashin tsoro da ke kara samu a tsakanin musulmin duniya karkashin albarkacin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran inda aka samu sauyin tunani da tafiyar da lamura wajen fuskantar azzaluman duniya Amerika da Yahudawan Sahayoniya da kuma ya haddasa rauni da kasawa ga Amerika da Yahudawan Sahayoniya.

362117

captcha