Bangaren Kasa Da kasa: nan bad a jimawa ba a birnin Barlin babban birnin Jamus za a bude cibiya ta musamman ta horar da tarbiyartar da limaman masallatai da kara masu sani kan addinin musulunci a cikin harshen Jamusanci.
Bayan ta nakalto daga banagaren labarai na kasa da kasa a Saudiya IINA ,cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa rahoton cewa: Alaksandre Faigar shugaban cibiyar koyar da limaman masallatai a Jamus ya bayyana cewa: bangaren koyarwa da malummai a cibiyar zai fara koyar da malummai da harshen Jamusanci kuma a karon farko za su ilimantar da masu tabligi da limaman masallatai ilmomin day a shafi addini da harshe Jamusanci.Ya kara da cewa: Matasa musulmi masu daukan karatu a cibiya na iyawa bayan kamala karatu su koyar a matsayin malumman addini a makarantu har ila yau da ci gaba da ayyukan tabligi da limamanci a masallatai. Alaksadre ya yi nuni da cewa wannan cibiya tana jiran amincewa a hukumce da limaman da suka horar a cibiyar kuma a farkon faraway ta sami talibai 32 kuma duk wanda ya kamala zai samu shahadar kamala karatu da hukumar ta amince karkashin ma'aikatar ilimi da tarbiya ta Jamus.
362176