Cibiyar koyar da Alkur'ani a iran Iqna bayan nakaltowa daga kamfanin dillancin labarai na Asosieted Press ta watsa rahoton cewa: A cikin wata wasika da aka bawa Weldez an bayyana masa cewa ba a amince da ba shi Vizas izinin shiga kasar Britaniya. A cikin wannan wasika an bayyana masa cewa: a Britaniya ana bukatar zaman lafiya da tsaro a tsakanin al'umma.Shi dai ya samu gayyata ne daga wani dan majalisar dokokin Britaniya don halartar wata kasuwar baje kolin fina-finai da zai nuna fim dinsa ta Fitina da a ciki ya ci zarafin Alkur'ani mai girma da sunan yancin fadin albarkacin baki da demokradiya kuma fim dinsa ta mintoci 15 ce.
362582