IQNA

A Karon Farko An Fassara Alkur'ani Da Yaren Kuramai

13:54 - February 14, 2009
Lambar Labari: 1744003
Bangaren kasa da kasa: Masu tarjama da fassarar Alkur'ani a cibiyar fassarar Al'kur'ani ta Malik Fahad a birnin Madina a karon farko sun fassara alkur'ani da yaren kuramai na ishara.

Cibiyar koyar da Alkur'ani a iran Iqna bayan ta nakalto daga jaridar almadina ta kasar Saudiya ta watsa rahoton cewa: Muhammad salim bin Shadid Al'aufi sakataren cibiyar kur'ani ta Malik Fahad amadina dangane da wannan labari ya bayyana cewa: tun da jimawa ne cibiyar ta dukufa wajen fassara Alkur'ni amma sai a wannan karo net a yi sa'ar fassara Alkur'ani da yaren kuramai kuma za a yada shi a cikin kasashen duniya domin amfani kuramai da duk wani da ke fahimtar yaren.Ya kara da cewa: cibiyar koyar da kuma fassarar Alkur'ani ta Malik Fahad ya bawa masu fassarar alkur'ani zuwa yaren Kuramai duk wani abut a fuskar na'ura da ilimi da suke bukata kuma nan bad a jimawa ba za su kamala daga karshe ya kara da cewa: wannan cibiya a shekara tana buga Alkur'ani kimanin miliyan goma a cikin yarurruka daban-daban kuma ya zuwa shekara ta 1429 hijiriya ta buga kimanin nau'in alkur'ani 230 da tarjumarsu a cikin yaruka daban-daban kkuma da wasu litattafai da suka kumshi Tarihin rayuwar manzon allah (SWA) da kaset-kaset na murya da na hotuna suna daga cikin abubuwan da cibiyar ke yi.

363359

captcha