Bangaren kasa da kasa: komitin koli na musulmin kasar Faransa CFCM ya fitar da wani bayani da a ciki yak e Allah wadai da rashin mutunta makabartar yahudawa a Montigny les Metz da ke wajen birnin Metz da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan ta nakalto daga Islamtoday ta watsa rahoton cewa: Muhamad Musawi shugaban komitin koli na musulmin Faransa a cikin wannan bayani bayan Allah wadai da wannan mataki na nuna wariya da kabilanci kan makabartar yahudawa a birnin Metz ya bukaci gwamnatin Faransa da ta doki mataki kan wadanda suka aikata wannan aiki da ya sabawa dan adam. Musawi ya kara da cewa: komitin koli na musulmin faransa na kiyayewa da mutumta rayuwa da matsayin sauran addinai da zaman lafiya da su da kuma fahimtar juna.Da fatar Allah ya sa a kama wadanda suka aikata haka na tona kaburburan yahudawa a wannan gari.
363395