IQNA

An gudanar da tarukan cika kwanaki Arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Sweden

10:24 - February 17, 2009
Lambar Labari: 1744836
Bangaren kasa da kasa: A daidai lokacin da ake gudanar da tarukan cika kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) a kasashe daban-daban, an gudanar da irin wadannan taruka a kasar Sweden.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Bratha) cewa; Nabil Shaki Taliqali, wakilin manyan malaman addini (Maraji'a) a nahiyar turai, ya jagoranci gudanar da tarukan cika kwanaki arba'in na shahadar Imam hussain (AS) a kasar Sweden, inda taron ya samu halartar dimbin masoya iyalan gidan manzon SAW da iyalan gidansa tsarkaka.

Bayanin ya kara da cewa an gabatar da jawabai a wajen taron da harsunan larabci da kuma yaren kasar Sweden, wanda shi ne yaren kasa da kowa ke fahimta.

364493
captcha