Cibiyar kula da harkokin kur'ani ta Ikna, ta nakalto daga shafin internet na (alakhbar Al-alam) cewa; kotun daukaka karar ta dauki wannan mataki ne bayan da mutumin ya amsa cewa shi ne ya tarjama kur'anin kuma ya kira shi tsakakakken kur'ani, ba tare da ya yi amfani da matanin larabci na asali ba. bayanin kotun ya ce an yanke hukunci ne kan mutumin mai suna ( Ahmad Gauth Zalmai) da kuma wanda ya taimaka masa ( Kari Moshtaq Ahmad) bayan da ya yi da'awar annabta, tare da raba kur'anin da ya fassara a matsayin littafinsa na annabta.
365175