Hujjatul Islama walmuslim Muhammad Rida Shahidi mai kula da shirya wannan gasar Olampik ta kasa da kasa kan karatul Alkur'ani da Hadisi a jami'ar almustapha (SWA) al'alamiya a tattaunawa da cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ya bayyana cewa; a bangaren gasar alkur'ani da hadisi akwai alkalai guda biyu Musin Musawi Balda da muhamad Situniya a bangaren Tajiwid yayinda Shahriyar Barhizgar da hujjatul Islam walmuslim Muhammad Haj Abu Kasim a bangaren hardar Alkur'ani sai kuma Abdulrasul Ibayi da Muhammad Husein Sa'idiyan a bangaren zakin murya sai kuma Ahmad Abu Kasim da mahmud Lutfi Niya a bangaren salo.
Ya ci gaba da cewa; a bangaren mata kuwa: Adib zade da Mir Giyashi a bangaren iya harda Shahid Fard da Abas Nazari a bangaren tajiwid sai jamali da Taufik Niya a bangaren salo yayin da Alwandi a bangaren murya suna daga cikin wadanda za su lura da alkalancin wannan gasa ta Alkur'ani bangaren mata.
366097