IQNA

Belgium Za Ta Dauki Bakuncin wani Taro Kan Dangantakar 'Ya'Ya Da Iyaye A Musulunci

8:42 - February 21, 2009
Lambar Labari: 1746355
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taro a kasar Belgium wanda zai yi dubi kan dangantakar 'ya'ya da kuma Iyaye a mahangar addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyoyin kungiyar (Islamic events) cewa; babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ce ta shirya taron. Bayanin ya ci gaba da cewa gobe Asabar ne za a gudanar da taron, wanda zai samu halartar masu nazari kan addinin musulunci da kuma masana daga kasar ta Belgium da ma wasu kasashen turai, inda za a yi bahasi kan wasu ayoyin alkur'ani da hadisai da suka yi bayani kan kyautata dangantaka tsakanin iyaye da 'ya'ya, da kuma tasirin hakan a cikin rayuwar zamantakewar al'umma.

366759


captcha