Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Aljazeera) ta kasar saudiyya cewa; shugaban kwamitin kula da ayyukan alkur'ani na kasar Saudiyya Aidah bin Ali Al'aufi, ya bayyana cewa samara da wannan sabuwar hanya zai taimaka ma mutane da dama da suke son yin amfani da internet wajen gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani, kama daga kira'a rubuce-rubuce kan kissoshi ko kalmomin da ke cikin kur'ani da dai sauransu, kuma an yi amfani da fasahar zamani ta na'ura mai kwakwalwa wajen shirya shafin.
366755