IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kwallon Tennis Tsakanin Sweden Da Isra'ila Ba Tare Da 'Yan Kallo Ba

8:39 - February 21, 2009
Lambar Labari: 1746360
Bangaren kasa da kasa: A gasar Wasannin Tennis na cin kofin (Divis Cup 2009) da za a gudanar a kasar Sweden, za a gudanar da wasa tsakanin Isra'ila da kuma mai masafkin baki Sweden ba tare da 'yan kallo ba saboda dalilan tsaro.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga gidan radiyon Oumma na kasar Sweden cewa; za a gudanar da wasa tsakanin Sweden da Isra'ila a ranar 6 ga watan Maris a gasar wasannin Tennis da za a gudanar a Sweden amma ba tare da 'yan kallo ba, saboda mahukuntan kasar ta Seweden sun tabbatar da cewa ba za su iya bayar da tabbacin tsaro ga 'yan wasan yahudawa ba, sakamakon yadda da dama daga cikin al'ummomin kasar suke nuna rashin amincewarsu da gudanar da wannan gasa tsakanin kasarsu da Isra'ila, sakamakon hare-haren da Isra'ilan ta kai kan al'ummar Gaza a 'yan lokutan baya.


366750
captcha