IQNA

Bahrain Za Ta Dauki Bakuncin Taron Saka Hannayaen Jari Bisa Tsarin Musulunci

9:21 - February 23, 2009
Lambar Labari: 1747450
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taron saka hannayen jari na duniya bisa tsarin musulunci a kasar Bahrain, bisa kulawar hukumar kula harkokin saka hannayen jari ta kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Bahrain (BNA) cewa; taron zai yi dubi a kan yadda musulmi masu saka hannayen jari za su ci gajiyar ayyukansu tare da kiyaye ka'idojin addini kan harkokin banki da saka hannayen jari a zamanance, kuma taron zai samu halartar masana kan harkokin banki da saka hannayen jari daga sassa daban-daban na duniya, bayanin ya kara da cewa hakan zai taimaka ma musulmi matuka, musamman idan aka yi la'akari da matsalolin tattalin arziki da a halin yanzu suka addabi duniya.

367665





captcha