IQNA

Malaman Addinin Kirista A Syria Sun Bukaci Benedict Da ya Janye Ziyararsa A Isra'ila

12:16 - February 24, 2009
Lambar Labari: 1748086
Bangaren kasa da kasa: Malaman addinin kirista na babbar majami'ar birnin (Homs) na kasar Syria, sun bukaci paproma Benedict na 16 da ya dakatar da batun ziyararsa a Isra'ila, sakamakon cin zarafin Annabi Isa (AS) da Maryam (SA)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sana na kasar Syria cewa; manyan malaman addinin kirista na babbar majami'ar Homs da ke Syria, sun bukaci Benedict na 16 da ya janye ziyarar da yake shirin kaiwa a Isra'ila, sakamakon cin zarafin annabi Isa (AS) da Maryam da yahudawan Isra'ila suka yi a cikin 'yan kwanakin nan.
Bayanin majami'ar ya ce; yahudawan sahyuniya bayan yin amfani da makaman da aka haramta a duniya wajen kashe dubban kananan yara da mata da tsoffi a zirin Gaza, yanzu kuma sun bage ga wulakanta tsarkakan abubuwa, da hakan ya hada da yin tozarci ga annabi Isa Al-masih (AS) da Maryam (SA) a kan haka suka bukaci Benedict da ya nuna fushinsa ta hanyar janye ziyarar tasa.

368278











captcha