Hujjatul Islam Muhsin Garuriyan mamba a komitin ilimi a babbar makaranta ta imam Khomeini ® a wata tattaunawa da bangaren ilimi na Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna kan Allah,Manzo da Alkur'ani ya bayyana cewa: Addinin musulunci shi ne addinin Allah kamar yadda haka lamarin yake a kullum muna danganta manzon da Allah a matsayin wanda zai isar da sakon Allah ga al'ummar duniya wannan shi ne ya sa a kullum daga an ambaci sunan ma'aiki yanada matsayi mai girma da dokaka a gurin musulmi kuma haka matsayin al'kur'ani yake .Bugu da kari manzon Allah shi ne babban abin koyi a gare mu kamar yadda ayar Alkur'ani ke cewa.
368017