Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Reauters) na kasar kasar Birtaniya cewa; taron ya gudana ne a birnin London, inda ya samu halartar masana daga kasashe daban-daban, da suka hada da masana kan harkokin banki da kuma manyan 'yan kasuwa musulmi da suke mallakar kamfanoni, gami da masu saka hannayen jari.
Kungiyar musulmin kasar Birtaniya ce ta shirya zaman taron, bisa la'akari da matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, wanda kuma kasashen musulmi na da babbar rawar da za su iya takawa wajen kwakkwafa matsalar yadda ba za ta shafe su sosai ba, kuma za su yi amfani da tsarin banki irin na Musulunci ne wajen fuskantar matsalar.
369039