Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa; sakataren kungiyar hadin kan duniya musulmi (Abdolaziz Bin Abdolmohsen Al-turki) ya fitar da wani da a cikinsa ya bayyana matsayin kungiyar kan shirin da aka watsa a wani gidan talabijin na Haramtacciyar Kasar Isra'ila na cin zarafi ga manzon Allah (SAW) wanda kuma kafin nan wannan gidan talabijin ya gabatar da wani shirin makamancinsa, inda ya ci zarafin annabi Isa (AS) da kuma Maryam (SA)
Al-turki ya ce tozarta annabawan Allah zai jawo fushin musulmi a duniya baki daya, kuma Haramtacciyar Kasar Isra'ila ita ce ke da alhakin duk abin da ka iya faruwa kan hakan.
369878