IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Matsayin Matasa A Rayuwar Zamantakewa A Indonesia

12:06 - March 01, 2009
Lambar Labari: 1749669
Bnagaren kasa da kasa: Za a gudanar da taro kan matsayin matasa da rawar da rawar da suke takawa a rayuwar zamantakewa a kasar Indonesia a shekara ta 2010.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; za a gudanar da taron ne tare da halartar manyan malamai na addinin muslunci da masana daga sassa daban-daban na duniya da ma'aikata a fagage daban-daban a kasashen musulmi.
A taron na kara wa juna ilimi kan matsayin matasa da rawar da za su iya takawa a rayuwa zamntakewa, masana za su yi bahasi kan irin turbar da ya kamata a dora rayuwar matasa musulmi, ta yadda hakan zai bar kyakkyawan tasiri a a nan gaba a cikin rayuwar zamantakewa a tsakanin msulmi, bisa la'akari da cewa matasa su ne kashin bayan kowace al'umma. Kamar yadda kuma taron zai yi nazari kan irin matsalolim matasa da kuma hanyoyin za a iya bi wajen warware su a ilmance da kuma a aikace.

370495
captcha