Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; bisa ga al'ada ana gudanar da taron girmama wadanda za su shiga cikin gasar kur'ani da hadisan ma'aiki kafin lokacin gudanar da gasar a masallacin jami'ar (Mas'ud Bin Abdulaziz) bayan kammala sallar Magriba.
Za a gudanar da gasar ne a bangarorin karatun kur'ani da kira'a daban-daban, kuma akwai bangaren harda, kama daga juzu'i na biyar har zuwa hardar dukkanin alkur'ani, kamar yadda za a gudanar da gasa a bangaren tajwidi da dukknin ka'idojinsa, kamar yadda za a gudanar da gasa a bangaren hadisi.
Yanzu haka dai adadin wadanda za su shiga cikin gasar ya kai mutane 47, gami da gogaggun alkalai
Wannan shi ne karo na goma sha shida da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar Saudiyya, kuma fara gudanar da ita ne a cikin shekara ta 1999.
370395