IQNA

Nuna Fim Din Fitina Ya Jawo Fushin Musulmin Kasar Amurka

12:01 - March 01, 2009
Lambar Labari: 1749672
Bnagaren kasa da kasa: Nuna Fim din fitina a congress din Amurka ya jawo fushin musulmin kasar, inda wasu daga cikinsu suka yi cincirindo a gaban ginin congress din.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam online) cewa; wani dan majalisar dattijan Amurka daga bangaren jam'iyar Repulican mai suna (John Kil) shi ne ya gayyaci dan majalisar kasar Holand din (Geert Wilders) mai tsananin gaba da addinin Musulunci da ya zo kasar Amurka domin nuna fim din fitina a Congress din Amurka, wanda a cikin fin din ya wulakanta alkur'ani mai tsari, da nufin wulakanta addinin Musulunci, lamarin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga musulmin Amurka da ma sauran musulmi a fadin duniya.

Ket Aleson wani dan majalisar wakilai ne a Amurka, wanda ya bayyana cewa shi mutum ne mai son fadin albarkacin baki, amma fin din fitina ba fadin albarkacin baki ba ne, tozarta addinin msulunci ne kawai.

370282

captcha