Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (AFP) cewa; alkalin kotun kasar Spain (Farnando Andro) ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da batun gurfanar da wasu jami'an sojin Isra'ila, wadanda suke da hannu kai tsaye wajen yin kisan gilla a kan palastinawa mazauna sansanin Jenin a shekara ta 2002. Daga cikin wadanda za a gurfanar din kuwa har da ministan yakin Isra'ila na wancan lokacin, da kuma manyan jamia'n soji takwas da bincike ya tabbatar da cewa su ne ke da hannu kai tsaye a kisan fararen hular Jenin.
A nasa bangaren ministan yakin Isra'ila Ehud Barack ya nuna rashin jin dadinsa dangane da wannan mataki na kotun kasar Spain, ya kuma bayyana fatan samun canji dangane da wannan matsayi.
360834