Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muhit ,cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ihsan Uglu ya bayyana cewa: cin mutunci da batanci da gidan talbijin na goma na gwamnatin HKI ta yi kan manzon Allah (SWA) bayan da a yan kwanakin na suka yi irin wannan cin mutunci da batanci kan Annabi Isa (AS) da Ma'aifiyarsa Maryam (AS0 sai gashi sun yi irin haka kan Annabin rahama (SWA) da hakan ya fito da hakikanin yanayin Yahudanci na nuna kyama kan sauran addinai . Ya kuma bayyana cewa ci gaba da haka wata manufa ce ta haddasa fitina ada rikici a tsakanin addinai a fadin duniya kuma da yardarm Allah ba za su cimma mummunar manufarsu ba.
370970