IQNA

14:10 - March 04, 2009
Lambar Labari: 1751717

Babban Muffin Kasar Masar Ya Bukaci Kafa Komitin Kasa Da Kasa Na Kare Kananan Kabilu Musulmi

Bangaren kasa da kasa: Ali Jum'a muffin kasar Masar a lokacin da yake ganawa da Nubadun jakadan kasar tailand a Masar ya bukaci kafa komitin kananan kabilu musulmi.

Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta nakalto daga jaridar Alwatana kasar saudiya ta kawo labarin Ali Jum'a na cewa: wannan hadin guiwa dole ya kumshi dukan wakilai daga kananan kabilu musulmi a fadin duniya da burin kare hakkin irin wannan kananan kabilu.Muffin ya kara da jaddada cewa: wannan komitin hadin kai da zummar taimakawa kananan kabilu musulmi da taimaka masu magance matsalolinsu kuma hakan zai kara habaka hulda a tsakaninsu.

372255
captcha