Bayan ta nakalto daga kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI ,cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ihsan Ikmalul Dine Uglu babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a lokacin bukin bude taron tattalin arziki a musulunce ya bayyana cewa: wannan taro wata babbar dam ace ga kasashen musulmi mambobi a wannan kungiya ta OCI na su samara da hanya mafi kyau da za ta dauki dogon lokaci tana taimakawa tattalin arzikin duniya musamman kasashen musulmi. Ya kara da cewa:siyasar kungiyar hadin kan kasashen musulmi tushenta na inganta yanayin tattalin arzikin kasashen musulmi ne da samara da hanyar da hakan zai tabbata cikin gaggawa don dongon dangantaka ta tattalin arziki da saye da sayarwa.
372195