Halartar Mahardatan Kur'ani Daga Kasashe 12 A Gasar Olympiyan Kur'ani Da Hadisi Ta Jami'ar Almustapha(SWA)
Bangaren da ke kula da harkokin alkur'ani: Ya zuwa yanzu mahardatan Kur'ani daga kasashe 12 ne suka samu halartar gasar jami'ar Almustapha (SWA) al'alami kuma wannan shi ne karo na 14 da shirya wannan gasa.
Muhammad Mahdi Sabagi shugaban komitin shirya wannan gasar karo na sha hudu ya bayyana cewa: ya zuwa yanzu an samu yan takara a wannan gasa daga kasashen Indiya, tailand ,Indonoziya,Nigeria,Kosovo,Tanzaniya,Pakistan,Turkiya,Azarbaijan,Komoro da Labanon da za su fafata da junansu kuma za a ji gaba da wannan fafatawa har zuwa mako mai kmawa a birnin Qum.