Bangaren Siyasa: A yayin gudanar da taron nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu a birnin Tehra, Ali Larijani ya bayyana cewa; kada Amurka ta yi zaton cewa za ta iya dakushe ruhin gwagwarmaya ba ta hanyar shirya taruka da tafiye-tafiye zuwa Palastinu da nuna goyon baya ga Isra'ila ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; shugaban majalisar shawara ta Iran Ali Larijani, ya fadi jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron goyon bayan al'ummar Palastinu cewa; kada Amurka ta yi zaton cewa za ta iya kawo karshen gwagwarmaya ko dakusheta ta hanyar tafiye-tafiyen da jami'anta ke yi zuwa Palastinu, tare da ci gaba da bayar da dukkanin goyon baya ga Isra'ila wajen ci gaba da danne al'ummar Palastinu, ya ce lokaci ya yi da Amurka za ta fahimci cewa bana ba bara ba ce, domin kuwa al'ummomin duniya sun farka, ba zsu kara fadawa tarkon da take dana musu a lokutan baya ba.
Daga karshe ya yi gudiya ga dukkanin wadanda suka karba kiran majalisar shawara ta Iran wajen halartar taron, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.
372913