Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (peninsula) cewa; Marubucin littafin nan mai suna lambun Musulunci kuma malami a jami'ar Texas a kasar Amurka (Safiyuddin Hamid) ya bayyana cewa; littafin nasa ya tabo ayoyi masu tabbatar da samuwar ubangiji ta hanyar yanayi da dabi'a, ya ce tarihin msulunci yana da fadi, domin kuwa an samu al'adu a wasu yankuna na kasashen turai tun tsawon shekaru da suka haura dubu daya, daga cikin wuraren da aka samu dadaddun abubuwa na al'adun musulunci kuwa har Spain, haka nan kuma an samu wasu abubuwan makamantan hakan a wasu biranan musulunci da suka hada da Sarmakand, Esfahan, Shiraz da dai sauransu.
Yanzu haka dai an fara gudanar da wani taro da ke halartar masana sama 20 daga kasashe daban –daban a birnin Doha nakasar Qatar, domin tattaunawa kan yanayin bincike da koyarwa a fagen kur'ani.
373003