Kamfanin dillancin labaran Ikan ya habarta cewa: a wani taro da aka gudanar a daren jiya a wani babban dakin taro da ke birnin Khartum na kasar sudan, shugaban majalisar shawara ta kasar Iran Ali Larijani ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa Amurka tana sin ta yin amfani da dammar da ta samu, bayan sun yi amfani da kotun duniya wajen fitar da sammaci kan shugaba Albashir, da ta yi fito na fito da al'ummar Sudan masu karfin zuciya da sadaukantarwa. Larijani ya ce Amurka ba za ta taba samun nasara kan al'ummar sudan ba.
Tun bayan kammala zaman taron goyon baya ga al'ummar Palastinu da aka gudanar a birnin Tehran, wata tawaga da ta kunshi jami'an Iran da na Syria gami da jagorin Hamas, suka kama hanya zuwa kasar Sudan, domin nuna goyon bayansu ga shugaba Albashir tare da yin watsi da hukuncin da kotun manyan laifuka ta duniya ta fitar kansa, bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a Darfur.
373940