Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga ofishin hulda da jama'a na majalisar fayyace tsarin musulunci a Iran ce Ayatullahi Hashimi Rafsanjani a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin Mali ya bayyana masa cewa: kasashen Iran da mali sun fadada dangantakarsu da huldar kasashen biyu kuma kasashen musulmi da sauran takwarorinsu masu tasowa na iyan samun ci gaba ta hanyar hada kai kuma ta wannan hanya ce za su fuskanci kasashe ma'abuta girman kai da danniya a duniya . A yau siyasar duniya na bukatar kasashen musulmi da su hada kansu domin kubutar da al'ummominsu daga zaluncin manyan kasashe.
375217