Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Shafin internet na cibiyar harkokin addinin Musulunci da ke birnin Washington na kasar Amurka, ta kawo wata makala ta musamman kan tarihin iyalan gidan manzon Allah (SAW) wanda a ciki ta bayyana cewa tarihin ma'aiki (SAW) cike yake da darussa ga rayuwa ta dan adam baki daya, rayuwa ce da take koyar da zamantakewa ta hakika, kyawawan dabi'u, 'yan adamtaka da karama.
Bayanin ya ci gaba da cewa idan aka dauki rayuwar ma'aiki ta zamantakewa a birnin Makka, za a fahimci kyawan dabi'u na 'yan adamtaka da manzon Allah ya nuna, bisa azbtarwa da cutarwa da ya yi ta fuskanta daga kafiran makka, da kuma yadda ya nuna darasin hakuri da juriya da dogaro ga ubangiji, wanda hakan ya zama babban madin nasara gare shi wajen isar da sakon Allah madaukakin sarki.
375965