Kamfanin dillancin labaran ina ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; Cibiyar da ke kula ayyukan masallacin Qods ta nuna matukar damuwarta dangane da gina wani ofishin 'yan sanda da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a cikin masallacin Qods, inda ta bayyana hakan da cewa wani mataki ne mai matukar hadari. A wani bayani da cibiyar ta fitar dangane da hakan ta bayyana cewa; yanzu haka Isra'ila ta fara aiwatar da shirin nata na gina wa 'yan sandanta ofishi a cikin masallacin Qods, duk da rashin amincewar da al'ummar musulmi na duniya ke nunawa kan hakan. Bayanin ya ce dole musulmin duniya su safke nauyin da ya rataya kansu wajen taka wa Haramtacciyar Kasar Isra'ila birki kan wannan mummunan aiki da ta fara gudanarwa.
376812