IQNA

An Gudanar Da Taron Maulidin Annabi (SAW) A Kasar Bangaladesh

14:35 - March 12, 2009
Lambar Labari: 1755294
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) a kasar Bangaladash a jiya talata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Bdnews) cewa; musulmin kasar Bangaladash sun gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) inda manyan malaman addinin musulunci suka gabatar da jawabai kan matsayin ma'aiki (SAW) da kuma yadda al'ummar musulmi za ta iya yin koyi da manzon Allah (SAW) a cikin dukkanin harkokin rayuwa. Rahoton ya kara da cewa a yayin gudanar da taron maulidin an kuma gudanar gasar karatun kur'ani mai tsarki, inda mahardata da kuma makaranta suka gudanar da gasa a fagagen karatu da kuma harda gami da tajwidi, an kuma bayar da kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara.

376606
captcha