Bangaren kasa da kasa: Wani kwamiti da aka kafa a Palastinu domin bincka kayan da Isra’ila ke sana’antawa da ake amfani da su, ya kammala gano kayyakin, da nufin haramta sayensu a cikin yankunan Palastinawa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Ma’an) cewa; Wani kwamiti da aka kafa a Palastinu domin bincka kayan da Isra’ila ke sana’antawa da ake amfani da su, ya kammala gano kayyakin, da nufin haramta sayensu a cikin yankunan Palastinawa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye. Rahoton ya ce kwamitin zai fadada ayyukansa ne a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma yankunan Zirin Gaza, ta yadda hakan zai taimaka wajen kaurace wa kayayyakin da Isra’ila take sana’antawa a cikin dkkanin yankunan palastinawa.
378068