IQNA

Musulunci Ya Zo Ne Domin Ya Yi Yaki Da Tsattsuran Ra'ayi

15:01 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756479
Bangaren kasa da kasa: Musulunci ya z one domin ya daidaita tunanin dan adam a cikin harkokin rayuwarsa, da hakan ya hada da kawar da tsattsauran ra'ayi da rikici kamar yadda kur'ani ya koyar da manzon Allah (SAW)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; shugaban majalisar malamai ta kasar Kamaru (Sa'id Ali Hamdou) ya bayyana cewa; Musulunci ya z one domin ya daidaita tunanin dan adam a cikin harkokin rayuwarsa, da hakan ya hada da kawar da tsattsauran ra'ayi da rikici kamar yadda kur'ani ya koyar da manzon Allah (SAW)
Ya ci gaba da cewa addinin Musulunci addini ne na fahimtar juna tsaklaninsa da sauran al'ummomi da sauran addinai, a kan haka a koda yaushe yana koyar da kyawawan dabi'u, tare da yin hani kan duk wani wuce gonad a iri a cikin tunani ku aiki, domin kuwa shi addini ne na rahma da ke nufin yaduwar wannan rahma ta ubangiji tsakanin dukkanin talikai.

378064




captcha