Bangaren siyasa da zamantakewa; Rarrabuwa da sabani a maimakon hadin kai da fahimtar juna ,jahilci da tsoro a maimakon ilimi da wayewa ko zalunci da rashin adalci a maimakon adalci sune manyan matsalolin da suke addabar al'ummar Manzo (SWA).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Rida azian shugaban da ke kula da ofishin yada al'adun Iran a ketare da ke zaune a Sera lanka a lokacin bukin Maulidi na Tunawa da ranar Haifuwar fiyayyan halitta Muhammadu dan Abdullahi (SWA) ya yi wannan bayani mai sosa raid a fayyace gaskiyar babbar matsalar da ke addabar kasashen musulmi a yau da cewa: Rarrabuwa da sabani a maimakon hadin kai da fahimtar juna ,jahilci da tsoro a maimakon ilimi da wayewa ko zalunci da rashin adalci a maimakon adalci sune manyan matsalolin da suke addabar al'ummar Manzo (SWA). Da jaddada cewa makiyan addinin musulunci na amfani da wannan matsala domin cimma burinsu kan musulmi yayin da rashin magance wannan matsala ya zunduma musulmin cikin wani mummunan yanayi da rashin tabbas na rayuwa da addini.
379019