IQNA

Al'ummar Musulmi Sun Yi Baki Guda Wajen watsi Da Hukumcin Kotun Duniya Kan Albashir

12:37 - March 26, 2009
Lambar Labari: 1758078
Bangaren siyasa: Jambe Islami a Jodan ta yi nuni da cewa: wannan mataki da kutun duniya mai zargin leifukan ta taimaka wannan kara hadin kan Al'ummar musulmi da Magana da yawu guda wajen kare shugaban kasar Sudan Albashir.
Daga Jodan ne cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta bayyana cewa: Jaridar Algad ta kasar ta jodan ta jiyo Hamza Mansur shugaban jabahatul Amal islami a wannan kasa yana cewa: hukumcin fitar da sammacin kama shugaban kasar Sudan Umar Albashir da kotun duniya mai tuhumar manyan leifuka ta yi ya karawa shugaban na Sudan farin jini a idon duniya kuma ya karawa duniyar musulmi kusanci da fahimtar juna a daidai wannan lokaci na zalumci da nuna wariya a fili karara.Mansuri ya kara bayyana cewa: wannan hukumci ba komi ban e face kara nuna wariya a kan musulmi da larabawa kuma za su ci gaba da adawa da wannan hukumci.

380264

captcha