IQNA

Wani Malamin Addinin Kiristanci Ya Yabi Musulmi Wajen Yada Addininsu

15:29 - March 28, 2009
Lambar Labari: 1758345
Bnagaren kasa da kasa: Babban malamin addinin kiristanci na majami'ar Canterbary ya yabi musulmi kan rawar da ya ce suna takawa wajen yada addininsu a cikin al'ummar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin (Muslim News) cewa; Dr Rwon Williams babban malamin addinin kiristanci na majami'ar Canterbary ya yabi musulmi kan rawar da ya ce suna takawa wajen yada addininsu a cikin al'ummar Birtaniya. Ya ce a ganinsa addinin musulunci da musulmi suna taka rawar gani wajen yada addini a cikin al'umma, wanda kuma hakan ko shakka babu yana da muhimmanci wajen wajen karkatar da tunanin mutane zuwa ga addini. A bangare guda kuma ya yi kakkausar suka dangane da yadda addini ya zama bako a cikin al'umma, ta yadda mai addini yak an zama daban tamkar wani bare a cikin al'umma ya ce wannan babban ci baya ne. A bangare guda kuma ya yaba da tatatunawar samara da fahimtar juna tsakanin addinai, kamar yadda ya nuna goyon bayan malaman addinin kiristanci na kasar Birtaniya wajen kai taimako ga al'ummar Gaza.

380570

captcha