IQNA

15:25 - March 29, 2009
Lambar Labari: 1758479

Wani Malami A Bolgaria Ya Soki Shirin Gwamnati Na Hana Saka Hijabi A Marantu

Bangaren kasa da kasa: Babban malamin addinin musulunci mai bayar da fatawa a kasar Bolgaria, ya soki lamirin gwamnatin kasar dangane da wani shirin da take nufin aiwatarwa na hana saka hijabi a makarantun kasar.

Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam online) cewa; babban malamin addinin musulunci mai bayar da fatawa a kasar Bolgaria, ya soki lamirin gwamnatin kasar dangane da wani shirin da take nufin aiwatarwa na hana saka hijabi a makarantun kasar. Malamin ya ce wannan manufa ta gwamnati wani yunkuri ne na danne hakkokin musulmin kasar tare da takura rayuwarsu, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin hakkokin dan adam da ma hakkokin addinansa.
A ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin kasar Bolgaria ta amince da wani daftarin kuduri na hana saka hijabin musulunci a makarantun kasar, amma ba za zartar da hakan ba har sai majalisar dokokin kasar ta amince da wannan daftarin kuduri, wanda hakan ne zai mayar da shi doka mai zaman kanta. Adadin musulmin kasar ya kai kashi 12 cikin dari, kuma ita ce kasa daga cikin kasashen tarayyar turai da ke musulmi akasarinsu 'yan asalin kasar ne.

380729

captcha