Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (alarabiya) ta kasar Syria cewa; An gudanar da wani taro kan batun bude reshen bankin musulunci da ke gudanar da mu'amalolinsa daidai da tsarin shari'ar addinin islama a kasar ta Syria. Rahoton ya kara da cewa babbar manufar gudanar da taron ita ce duba hanyoyi da suka fi dacewa wajen kyautata mu'amala tsakanin al'ummar kasar daidai da ka'ida irin ta shari'ar musulunci kasantuwarsu mabiya addini musulunci, wanda kuma hakan zai bayar da dama ga mau kauracewa tsarin mu'amalar ta banki saboda tsoron cin riba su shiga cikin harkar bayan kiyaye ka'idojin addinin a ckin harkoki, tare da yin amfani da wannan damar wajen karfafa harkokin tattalin arzikinsu, wanda ci gaban da hakan zai kawo ba zai takaitu ga mutanen ba, a a hakan ci gaba ne ga al'ummar musulmi da gwamnatocin kasashensu.
381430