Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar jaridar Alshark Ausat ta kasa da kasa ta watsa rahoton cewa:wannan taro da ke samun sa idon Muhammad Jasir shugaban muassisar bayar dab shi a kasar Saudiya ya samu halartar masana masu yawan gasket daga kasashen musulmi da kuma shugabannin bankoki 56 na kasashen musulmi.Mahalrtar wannan taro sun nuna niyarsu ta aiki gadan-gadan kuma tare da bada hadin kai a tsakanin kasashen musulmi ta fanning tattalin arziki da ayyukan banki.Har ila yau kuma sun bayyana aniyarsu ta kiyaye dokokin banki da kuma gudanarwa.
381691