Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Nasij ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ta watsa rahoton cewa:a wannan taro na karramawa an karrama shugabannin makarantu da jagororin gidajen koyar da Alkur'ani da Sunna a arewacin yankin Gaza da kuma wani bangare na shugabannin da ke kula koyorwa da kuma ilmantar da yara a yankin.Abdul Aziz faris daya daga cikin shugabannin makarantu a gaza ya jaddada wajibcin kula da koyar da Alkur'ani da hardarsa da kuma tusa so da kaunar hardar Kur'ani a tsakanin yara kanana.Da dama daga cikin malummai da shugabannin makarantun kur'ani na yara a yankin sun gamsu da yadda ake shirya gasa ta hardar Kur'ani a tsakanin yara kanana da yadda ake samun karbuwa daga yara da uwayensu.
381680