IQNA

Babban Jagora Kan Tattali Za A Iya Samunsa A Cikin Ayyoyin Kur'ani

13:38 - April 07, 2009
Lambar Labari: 1761552
Bangaren zamantakewa: Karkashin fadar Malam Suleimiyan babban misali sahihi kan tattali yana cikin ayoyin kur'ani Kuma Allah Madakakin Sarki ya yi mana Bushara da rayuwa mai inganci madaidaiciya matukar muka yi aiki da haka.
Malam Suleimiyan KhudaMurad malami a hauzar birnin Qum a wata hira da cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ya yi bayani a fili cewa: Aiwatar da taken yin tattali da hana almubaziranci a tsakanin jama'a zai tabbatar da adalci a rayuwa ta zamantakewa da samara da kwanciyar hankali a tsakanin jama'a. a ci gaba da bayaninsa ya yi nuni da koyarwa ta Alkur'ani da cewaa; Islah,salihda maslah suna daga cikin kalmomin da kur'ani ya yi amfani da su wajen jan hankali domin gyaran al'umma kuma wannan yana daga cikin burin bayyanar Mahdi (AJ).Mamba a cikin komitin malumman Hauza a birnin Qum ya kara da cewa; a daidaiku ko a jama'ance ana bukat gyara da daidaita al'umma kuma a tare ne za a iya cimma wannan burin a tattali da gyara a cikin al'umma.Har ila yau ya yi nuni da hangen nesan jagoran juyin juya halin musulunci day a bawa wannan shekara wannan suna domin yin daidaito ta fuskar almubazziranci da aka yi a shekarun baya.

383669

captcha