IQNA

17:19 - April 08, 2009
Lambar Labari: 1762211

An Kafa Wata Cibiya Mai Suna Yaren Kur'ani A Bangaladesh

Bangaren kasa da kasa: Bankin musulunci ya kafa wata cibiya mai suna yaren kur'ani a birnin Daka na kasar Bangaladesh da nufin koyar da mutane ma'anonin kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyiyon bankin musulunci reshen kasar Bangakadesh cewa; bankin musulunci ya kafa wata cibiya mai suna yaren kur'ani a birnin Daka na kasar Bangaladesh da nufin koyar da mutane ma'anonin kur'ani mai tsarki. Abdul Hazan shi ne tsohon managing darakta na bankin musulunci a kasar Bangaladash, ya kuma bayyana cewa babbar manufar kafa wannan cibiya ba ta wuce koyar da musulmin kasar ma'anonin kur'ani mai tsarki ba, domin kuwa a cewarsa cibiyar ta tanadi dukkanin kayan aiki na koyarwa ko nazari, ga masu bukatar shiga aji za su iya yin rijista su shiga azuzuwa domin koyon karatu da sauran ilmomin kur'ani, ga masu son yin nazari kuma, an tanadi manyan dakunan karatu da zasu iya duba littafai da suke bukata domin samun karuwa a fagagen ilmomin kur'ani da ma addini baki daya.

384231



captcha