IQNA

Wasu Cibiyoyin Amurka Na Raba Kur'anai Marassa Inganci A Kuwait

13:59 - April 09, 2009
Lambar Labari: 1762422
Bangaren kasa da kasa: Cibiyoyin buga littafai na kasar Amurka wato (Omega 2001) da kuma (Win Press) sun buga wani kur'ani maras inganci mai suna (Furqanul Haq) kuma sun fara raba shi a kasar Kuwait da nufin karkatar da tunanin musulmi daga sakon kur'ani na gaskiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Alhakika Dauliya) ta kasar Jordan cewa; shahararrun cibiyoyin buga littafan nan na kasar Amurka wato (Omega 2001) da kuma (Win Press) sun buga wani kur'ani maras inganci mai suna (Furqanul Haq) kuma sun fara raba shi a kasar Kuwait da nufin karkatar da tunanin musulmi daga sakon kur'ani na gaskiya. A ci gabatarwar da aka rubuta a farkon kur'anin da cibiyoyin biyu suka buga, an bayyana cewa an shirya shi ne domin amfanin duniyar musulmi musamman ma kasashen larabawa. Tuni Amurkawan suka fara raba wannan kur'ani a makarantun 'yan kasashen waje dake kasar Kuwait. Kur'anin amurkawan dai an buga shi ne a cikin shafuka 366, kamar yadda ya kunshi surori 77 sabanin kur'ani wanda Allah ya safkar wa manzonsa. Acin wasu bangarorinsa an yi kokarin juya ma'anar wasu ayoyi da ke cikin kur'ani mai tsarki domin kawo rudani dangane da sahihiyar ma'anarsu. Jaridar ta ce wannan wani yaki ne na rowan sanyi cibiyoyin na Amurka suka shelanta akan addinin musulunci, wanda kuma bai kamata al'ummar musulmi ta yi shiru kan hakan ba.

384936


captcha