IQNA

An Fassara Littafin Nahjul-Balagha A Cikin harshen Sawahili

13:57 - April 09, 2009
Lambar Labari: 1762424
Bangaren al'adu da fasaha: An fassara littafin Nahjul-balagha a cikin harshen Sawahili a kasar Tanzania, kuma nan bad a jimawa ba za fitar da shi tare da yada shi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a kokarin da cibiyar kula da al'adu da yada koyarwar musulunci ta kasar Iran take yi a kasashen ketare, an fassara littafin Nahjul-balagha a cikin harshen Sawahili a kasar Tanzania, kuma nan bad a jimawa ba za fitar da shi tare da yada shi. Tun kimanin watanni uku da suka gabata ne aka fara gudanar da aikin fassarar littafin Nahjul-balagha a cikin harshen sawahili a kasar Tanzania, inda ofishin yada al'adu da koyarwar musulunci dake birnin darsalam fadar mulkin kasar Tanzania ya shiga gaba wajen gudanar da aikin tarjamar, kuma nan da 'yan kwanaki masu za a fitar da shi, tare da raba shi a cibiyoyin ilimi da al'adu na kasar da ma sauran kasashe da suke Magana da harshen Sawahili, kamar yadda za a iya samunsa a kasuwa domin sayarwa jama'a masu bukatar karantawa.

384991

captcha