Bangaren kasa da kasa: Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO, ta kayi kakkausar suka dangane da yadda Haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da gina ramuka karkashin masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO, ta kayi kakkausar suka dangane da yadda Haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da gina ramuka karkashin masallacin Qods mai alfarma. Kungiyar ta yi wannan suka ne a lokacin da take gudanar da taro karo na biyu kan gina ramuka da Isra'ila ke ci gaba da yi a karkashin masallacin Qods mai alfarma, an dai gudanar da wannan taro ne a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda ya samu halartar mambobin kungiyar daga kasashe daban-daban na musulmi. Bayanin bayan taro da kungiyar ta fitar ya kirayi gwamnatin yahudawan sahyuniya da ta gaggauta dakatar da ta'asar da take tafkawa da nufin rushe masallacin QODS kowa ya rasa, bayanin ya ce wannan mummunan aiki ne da ya zama wajibi ya kawo karshe cikin gaggawa.
385696