IQNA

15:59 - April 13, 2009
Lambar Labari: 1764386

Annabi Muhammad (SAW) Shi Ne Babban Jagoran Na Siyasa A Tarihi

Bangaren kasa da kasa: Marubucin nan dan kasar Amurka Mikel Hart ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da tarihin Musulunci tun daga lokacin bayyanarsa, za mu fahimci cewa Muhammad shi ne babban jagora na siyasa a tarihi.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin kamfanin dillancin labaran Mohit cewa; marubucin nan dan kasar Amurka kuma masanin tarihi Mikel Hart ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da tarihin Musulunci tun daga lokacin bayyanarsa, za mu fahimci cewa Muhammad shi ne babban jagora na siyasa a tarihi. Marubucin ya ci gaba da cewa idan muka dubi yadda salon da Muhammad ya yi amfani da shi wajen yada addininsa, za mu fahimci cewa lallai shi jagora ne a dukkanin bangarori, domin kuwa mutum ne mai matukar hangen nesa, da yin amfani hikima wajen gudanar da lamurransa, wanda hakan ya sa Muhammad ya zama jagora ba wai kawai ta bngaren addini ba, a'a har ma ta bangaren harkokin duniya, kuma dabi'unsa da salon tafiyar da lamurransa ya sanya shi ya zama maras na daya a tarihin duniya.

386676
captcha