IQNA

17:11 - April 13, 2009
Lambar Labari: 1764424

Amirin Makka: Birnin Makka Zai Zama Birni Mafi Kyau Na Zamani A duniya

Bangaren manema labarai: Said Ja'afar Fatimi Nush Abadi; Tare da la'akari da daddeden tarihin birnin Makka da kuma kasancewarsa birnin musulunci za mayar da shi birni mafi kyau a duniya.

Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: majiyar da ke watsa labarai da suka shafi Hajji ta bayyana Khalid Alfaisal amirin birnin Makka ya yi nuni da sabbin shirye-shirye irin na zamani da za su taimaka matuka gaya wajen sakewa birnin tsari da yanayi da hakan zai ba shi damar zama birni mafi tsari da kyau irin na zamani a duniya a yau.har ila yau ya kara da cewa kasancewarsa mai tsawon tarihi da kasancewarsa birnin musulunci amma za a yi masa tsari irin na zamani da zai bambanta shi da sauran biranai a duniya.


386483
captcha