IQNA

Kur'ani Majid Shi Ne Babbar Madogara A Wannan Duniya Da kuma Yaki Da Fasadi

17:56 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1766977
Bangare kula da harkokin kur'ani : Duk wani bayani kan tattalin arziki da magance matsalar fasadi da ta tattalin arziki da duniya ke fuskanta za a iya magance tat a hanyar yin dogaro da kur'ani mai girma.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo Ayatullah nasir Makarimul Shirazi daya daga cikin manyan malummai da ake takalidinsu a cikin wani sako day a aika yana cewa; a cikin wannan duniya da ke ciki da sharri da fasadi da kuma matsaloli barkatai na madda da ma'anawiya da kuma rikicin da duniyar ke fuskanta na tattalin arziki na baya-bayan nan za a iya magance su idan aka yi aiki da umarnin alkur'ani mai girma . Kuma a yau musulmi bas u da wani zabi face yin aiki da kuma riko da kur'ani mai girma da kuma fadar Allah da ma'aikinsa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa.

390153

captcha