IQNA

Kusanto Da Mazhabobi Ba Ya Nufin Sunna Su Koma Shi'a Ko Shi'a Su Koma Sunna

17:37 - April 21, 2009
Lambar Labari: 1768141
Bangaren siyasa da zamantakewa: Wajibi ne da yakamata malamai dam asana su san da shi kan cewa, ma'anar kusanto da fahimtar juna tsakanin mazhabobin musulunci, ba yana nufin sunna su koma shi'a ba ne ko kuma shi'a su koma sunna.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen birnin Qom ya habarta cewa; a cikin wani bayani da daya daga cikin manyan malaman addinin musulunci da ake komawa zuwa zuwa gare su a Iran Ayatollah Ja'afar Sobhani ya gabatar, ya bayyana cewa; wajibi ne da yakamata malamai dam asana su san da shi kan cewa, ma'anar kusanto da fahimtar juna tsakanin mazhabobin musulunci, ba yana nufin sunna su koma shi'a ba ne ko kuma shi'a su koma sunna. Ya ci gaba da cewa batun bahasin mazhaba ba batu ba ne na mutanen gari, batu ne da ya kebanci malamai dam asana kan addini, saboda haka ya kamata malamai su ajiye duk wani shakku kan wajibcin hada kai tsakanin al'ummar musulmi, domin kuwa hakan bay a nufin wani bangare ya ajiye akidarsa ya zo ya bi akidar daya bangare.

391536


captcha