A cikin Wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da shugaban kungiyar lauyoyi ta kasar Senegal kuma shugaban bangaren shari'a na jami'ar Dakar Amustu Susid ya bayyana cewa; Rashin yin aiki da dokokin kasa da kasa daga bangaren manyan kasashen duniya, ya saka al'ummomin cikin shakku dangane da gaskiyarsu wajen babatun kare ka'idoji da dokokin kasa da kasa. Ya ci gaba da cewa rashin girmama dokokin kasa da kasa da kasashen duniya musamman ma manyan daga cikinsu ba su yi, ya sanyta dokokin ba su da wata kima a idon al'ummomin duniya. Ya ce ya kamata ce a ce dokokin da ake kafawa da ka'adojin da ake shimfidawa a matsayi na kasa da kasa kowace kasa ta yi aiki da su, kuma dole ne a gudanar da su a kan kowace kasa, maimakon kebance wasu kasashe su zama birbishinsu, ko kuma su zama 'yan lele da ba a iya hukunta su a kan dukkanin tabargazar da suke aikatawa kan al'ummomin duniya.
394131